Luke 23

1Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. 2Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da alʼummarmu. Yana hana a ba wa Kaisar haraji. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.”

3Sai Bilatus ya tambayi Yesu, ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

4Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron, ya ce, “Ni fa, ban sami wani tushen zargi game wannan mutum nan ba.”

5Amma suka nace, suna cewa, “Yana ta da hankulan mutane, a koʼina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi kuma har ya kai nan.”

6Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?” 7Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin kuwa Hiridus yana Urushalima.

8Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi. A kan abin da ya ji game da shi, ya yi fata ya ga Yesu, ya yi waɗansu ayyukan banmamaki. 9Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai bashi ko amsa ba. 10Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa. 11Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa baʼa. Saʼan nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus. 12A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.

13Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, 14ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. 15Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa. 16Saboda haka, zan hore shi, saʼan nan in sāke shi.” 17(A kowace Biki, dole ya saki mutum ɗaya daga kurkuku.)

18Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”

19(Barabbas yana kurkuku saboda laifin ta da hankali a birnin, da kuma don kisankai.) 20Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. 21Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, saʼan nan in sāke shi.”

23Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi. 24Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu. 25Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda ta da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Saʼan nan ya ba da Yesu ga nufinsu.

Gicciyewa

26Saʼad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya. 27Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makomi da kuka dominsa. 28Yesu ya juya, ya ce musu, “ʼYan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ʼyaʼyanku. 29Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’ 30Saʼan nan,

“ ‘za su ce wa duwatsu,
“Ku fāɗi a kanmu!”
Za su ce wa tuddai kuma,
“Ku rufe mu!” ’
Hos 10.8

31Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?”

32Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye. 33Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuriʼa.

35Mutanen suka tsaya suna ƙallo. Har masu mulki ma suka yi masa baʼa, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

36Sojoji su ma, suka zo suka yi masa baʼa. Suka miƙa masa ruwan tsami. 37Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

38Bisa da shi kuma akwai wani rubutu da ya ce, “WANNAN SHI NE SARKIN YAHUDAWA.” 39Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi, ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”

40Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi, ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

42Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni saʼad da ka shiga mulkinka.”

43Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

Mutuwar Yesu

44Yanzu kuwa wajen saʼa ta shida ne, kuma duhu ya rufe koʼina a ƙasar, har zuwa saʼa ta tara, 45domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu. 46Yesu ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.

47Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah, ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.” 48Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi. 49Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna ƙallon abubuwan nan.

Binne Yesu

50Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci, 51shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah. 52Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba. 54An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa.

55Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin. 56Saʼan nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.

Copyright information for HauSRK